IQNA

Sayyid Nasrallah Ya Gana Da Babban Sakataren  Jihadul Islami Kan Halin Da ake Ciki A Zirin Gaza

15:52 - August 24, 2022
Lambar Labari: 3487740
Tehran (IQNA) Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah ya karbi bakuncin babban sakataren kungiyar Islamic Jihad a Palastinu Ziad Nakhaleh a birnin Beirut na kasar Lebanon.

Sayyid Nasrallah da Nakhaleh sun yi nazari kan abubuwan da suka faru a baya-bayan nan  a yankunan zirin Gaza da yammacin kogin Jordan, tare da yin dubi a kan yakin da aka yi da Isra'ila ta kaddamar kan yankunan Falastinawa a kwanakin baya-bayan nan.

Sun kuma tattauna batutuwan da suka shafi fagage na siyasa a bangarori  daban-daban na yankin, da kuma rawar da ake sa ran bangarorin daban-daban za su taka a fagen gwagwarmaya  a mataki na gaba wajen tunkarar zalunci da mamayar Isra’ila a Falastinu, da kuma ayyukanta na tsokana da wuce gona da iri a kan wasu kasashen larabawa na yankin.

 

4080496

 

 

 

 

captcha